Tsaro
Wani Babban Taimako Da Jami’an Tsaron Nijar Suka Yiwa Daukacin ‘Yan Najeriya.
Jami’an Tsaron Nijar sun kama Matasa Biyu Masu Safarar Makamai daga Jamhuriyar Nijar Zuwa Jahar Sokoto a Najeriya.
Rundunar Jami’an tsaro na garin Maradi sunyi gagarumin kamu.
Rundunar Jami’an tsaro na gendarma na guidan rumji dake jahar Maradi sunyi nasar cabke wasu mutane dauke da muggan makamai na yaki, bindigogi da harsashai.
Masu dakon makaman dai nada zummar tsallakawa dasu ne a tarayyar nageria.
Jami’an dai sunyi gangamin shelantawa al’umma na Jihar ta maradi nasarar da suka samu, inda suka gabatar da wadanda aka Kama din tare da makaman ga gomnan jahar ta Maradi da sauran manya masu ruwa da tsaki a harkar ta tsaro na Jihar.