Wani Fasto Dan jihar sokoto mai suna Mathew kuka ya ce da wani kiristan Arewa ne yake mulkin Najeriya kuma ake wannan ta’addancin a yanzu da tuni an yi masa juyin mulki.
Mathew kuka ya yi wannan bayani ne a ranar idin su Na kirsimati, inda yake cewa gwamnatin Najeriya ta ci amanar ‘yan Arewa mabiya addininsu na kirsta ta hanyar sayar da ruhin su ga ‘yan ta’addan da suke cigaba da ta’addanci a Arewacin Najeriya don jaddada boyayyiyar manufarsu ta kafa gwamnatin musulunci a Najeriya.
Mathew kuka ya ce yawan kashe kashe da zubar da jinin da ke cigaba da faruwa a Arewacin Najeriya yunkuri ne Na kafa gwamnatin musulunci a Najeriya
Mathew kuka ya cigaba da cewa duk wani Dan Najeriya mai son gaskiya ya san babu yadda za ai ace wani shugaban kasa Dan Arewa Wanda ba musulmi ba a lokacin Sa a samu ta’adi da muguwar barna kamar yadda ake samu a yanzu sannan ace ba a kifar da gwamnatin Sa ba, da tuni sojoji sun yi masa juyin mulki ko kuma kasar ta fada cikin rikicin addini mai tsanani.
Mathew kuka ya kara da cewa amma gwamnatin nan tana zaton kiristoci bazasu iya daukar matakin komai bane, kamar suna zaune ne haka kawai, to ba zai yiwu ba.
Mathew ya yi wannan raddi da wannan bayani ne bisa kashe wani Dan uwansa mai matsayin Fasto da ‘yan ta’addan sukai a sokoto amma ba tare da gwamnati ta dau wani mataki ba.
Daga Kabiru Ado Muhd