Wani Gwamnan Arewa Ne Kwamandan Boko Haram Inji Tsohon Mataimakin Shugaban CBN.

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe
Tsohon mataimakin shugaban babban bankin Najeriya, CBN, Obadia Mailafiya ya bayyana cewa, wani gwamnan Arewa ne kwamandan Boko Haram.
Mailafiya yayi wannan ikirarine yayin da ake tattaunawa dashi a wani gidan Rediyon me suna Nigerian Info, kamar yanda Hutudole ya rawaito, kuma yayi wannan magane a yayin da yake sharhi kan rikicin kudancin Jihar Kaduna.
Ya bayyana cewa an samu wannan labarine daga bakin wani babban kwamandan kungiyar da ya tuba. An tambayi Mailafiya kan yanda Gwamnan Kaduna yayi martani akan rikicin.
Sai ya kada bami yace ai irin yanda gwamnatin tarayya tace wani fadan saukar fansa ne ba tare da yin wani abuba shima gwamnan jihar ya bayyana haka, to ya nuna cewa suna da hannu a rikicin, hutudole ya kawo muku cewa, Mailafiya ya kara da cewa bari ya fasa kwai, yace suna hanyar samun bayanan sirri kuma sun zauna da wasu kwamandojin kungiyar Boko Haram ba sau daya ba ba sau biyu ba.
Yace sun gaya musu cewa wani gwamnan Arewa ne ke daukar nauyin mayakan Boko Haram din. Hutudole ya kawo muku cewa, Mailafiya Yace Boko Haram da ‘yan Bindiga duk abu daya ne kuma sun rika zirga-zirgar su duk da ana cikin kulle.