Al'adu

Wani Labari Mai Sosa zuciya Wata Rana Marigayi Sarkin Kano Ado Bayero.

Spread the love

Ance wata rana sarkin Kano Ado ya dawo daga tafiya, ya biyo ta Katsina Road, sai yake cewa Sarki Waziri (Danrimi), akwai wani gida na anan, da na mallaka tun kafin in zama sarki, amma ban kara waiwayarsa ba, ban sani ba ko zan gane shi?! Sarki Waziri yace ” Allah ya taimaki sarki, sai inzo in duba” sarki yace “gidan kane? Gida nane, zan zo in duba kayana da kai na.

Bayan yan kwanaki, rannan da dare sai sarki ya sa aka kira masa Danrimi, yace masa yazo ya raka shi unguwa. Suka tafi, Danrimi na jan mota, sai Katsina Rd, su shiga nan, su shiga nan, har suka zo daidai wani gida. Sarkin Kano ya umarci Danrimi ya tsaya, yace masa “ai kuwa wannan ne gidan, tabbas”

Suka fito, suka saka akayi musu sallama da maigidan cikin dare. Maigidan ya fito, suka gaisa. Sarkin Kano ya kalle shi yace ” wannan gidan ka ne?” Yace “eh” yace masa saya kayi ko kuma baka akayi? Yace gaskiya asali gidan mahaifinmu ne muka gada. Sarki yace masa ” kai dan wane ne( ya fadi sunan maigidan), yace eh. Kafin ya mutu bai bar muku wasiyya ba? Sarki ya tambayi maigidan. Yace “eh ya bar mana wasiyya, yace gidan nan na wani mutum ne Malam Ado”.

Sarki yace masa ” to nine malam Ado, kuma ba zuwa nayi don in tashe ku ba, na sayi wannan gida sama da shekara 40 da suka wuce, kuma ni na saka mahaifinku a ciki, Amma abinda nake so da kai, gobe kazo fada, muje gaban sarki da kai, saboda a tabbatar da wannan magana, komai ayi shi da hukuma yafi amfani. Amma kar ka ji komai, ba tashinku zanyi ba”. Maigidan ya amsa yace “to Allah ya kaimu”. Sarki yace masa, In kazo ka nemi Sarki Waziri, zai kaimu gaban sarki da kai, sai a tabbatar da maganar.

Da safe maigida ya tafi fada, yaje ya nemi Sarki Waziri, aka kai shi office din sarki waziri. Ya gabatar da kansa, sarki Waziri yace ” kaine?” Yace “eh nine” yace “to jira”

Da sarki ya zauna a fada aka kira bawan Allan nan, shi dai yana ta zura ido baiga malam Ado ba. Har aka kai shi gaban sarki.

Sarki yace masa ” kaine muka je gidan ka jiya?” Mutum ya gyara zama, ya kasa magana, saboda bai taba zaton Malam Ado sarkin Kano bane. Sarki yace masa ” to nine malam Ado. Gida nane. Ni na saka mahaifinku a ciki. Kuma mun ji dadi da ka rike wasiyyar mahaifinka. (Shi dai mutum yayi kasake, ya kasa cewa komai). Sarki yace ” Allah ya shi ma albarka”. Nan da nan fada ta dauka ” Allah ya shima albarka inji sarki”!!!!

Sarki yace ku nawa ne mahaifinku ya bari, yace ” mu bakwai ne: uku maza hudu mata” sarki yace “to yanzu in aka bar maka wannan gida an hada ka rigima da yanuwanka, saboda haka; kaje ka nemo gida a saya maka, su kuma kannenka maza a bar musu wannan gidan su raba. Yanuwanka mata kuma , ku kula dasu, kar ku bar su; su shiga wani hali.

Ance mutumin nan, saboda murna a kasa ya koma gida.

Allah ya jikan sarkin Kano Ado, Allah ya karfafi bayansa.

Daga Usman A Usman

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button