Rahotanni

Wani magidanci yayi garkuwa da ‘yar da A Jihar

Spread the love

Wani dan asalin jihar Kano, Fahad Ali, ya shiga hannun ‘yan sanda tare da gurfanar da shi a gaban kotun majistare da ke zamanta yankin hajji kan zargin sace’ yarsa ‘yar shekara hudu da haihuwa tare da neman kudin fansa N2m daga matar, uwar yarinyar

Mai gabatar da karar ya fadawa kotu cewa Shamsiyya Mohammed, mahaifiyar yarinyar, ta kai kara ga ‘yan sanda cewa a ranar 29 ga Satumbar, 2020 aka sace‘ yarta kuma bayan wani lokaci mai garkuwan ya kira ta a waya yana neman ta biya kudin fansa N2m ko kuma a kashe yarinyar. Bayan bincike na makonni biyu, ‘yan sanda sun gano cewa mijinta, Fahad Ali, mahaifin yarinyar ne ke wannan irin kiranyen kamar yadda aka samu yarinyar da aka sace tare da shi. Ali ya musanta aikata laifin a lokacin da aka karanta masa tuhumar a kotun.

Alkalin kotun, Sakina Aminu, ta ba da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake zargin a gidan yari har zuwa ranar 24 ga wannan watan domin ci gaba da sauraron shari’ar

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button