Labarai

Wani magidanci yayima Yara Goma Fyade a maraban Nyanya

Spread the love

An gurfanar da wani magidanci Mai suna Adamu Umar Dunomo Mazaunin Unguwar Rugar Juli dake yankin Maraba a karamar Hukumar Karu a gaban babar kotun Majistare dake kasuwa Mahammadu Buhari International Market Maraba bisa zargin aikata laifin fyade ta hanyar Luwadi ga kananan yara maza su Goma masu kimanin shekara 4, 7, 10, 12 binciken mu ya tabbatar da duka yara basu haura shekara 17 ba.

Dan sanda Mai gabatar da kara Mr. Nanzi ya fara gabatar da Wanda ake zargi da aikata laifin ranar 31 ga watan Augustan 2020 daga nan kotu ta ajjiye shi a Gidan yarin suleja har zuwa yau ranar litinin 28 ga watan Satumbar 2020 inda aka samu akasin kawo Wanda ake zargin kotu a Kan lokaci Wanda a lokacin kotun ta tashi a zaman ta na yau

Wasu daga cikin iyayen yara da aka yiwa fyaden da Shugaban mazauna unguwar Alhaji Aliyu Ahmad Janyau, sun yi kira ga kungiyoyi masu zaman kansu da Uwrgidan Gwamnan Jihar Nasarawa Hajiya Salifat Abdullah A. Sule su shigo lamarin dan tabbatar da an hukunta Mai laifin

Alkalin Kotun Mai Shari’a Hauwa Onu Osa, ta dage sauraron sauraron karar zuwa litinin 26 ga watan Oktoban 2020 madogara Tambari Online hausa

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button