Rahotanni

Wani Mahaifi Ya Kulle Dan Shi Shekaru 35 A Kano.

Spread the love

Muhammad, mazaunin Kofar Fada a karamar hukumar Rogo ta jihar Kano, ‘yan sanda da cibiyar kare hakkin dan adam sun kubutar da shi a yau Alhamis a nan Rogo.

‘Yan sanda sun kubutar da Murtala Muhammad, dan shekara 55, a cikin garin Kano bayan da mahaifinsa ya kulle shi a wani daki tsawon shekara 30.

Muhammad, mazaunin Kofar Fada a karamar hukumar Rogo ta jihar Kano, ‘yan sanda da cibiyar kare hakkin dan adam sun kubutar da shi yau Alhamis.

An ce wanda aka azabtar an daureshi ne saboda rashin lafiyar kwakwalwa da yake fama da Shi.

Muhammad ya ce yana farin ciki da aka kubutar da shi.

Comrade AA Haruna Ayagi, Daraktan zartarwa na Kungiyar Kare Hakkin Bil-Adama, ya ce Muhammad ya cika shekara 25 da haihuwa lokacin da aka Garkame shi a gidan.

Wannan na zuwa ne kwanaki hudu bayan da ‘yan sanda suka kubutar da Ibrahim Lawan, wani mutumin da mahaifinsa ya garkame shi shekaru 15 a Kano.

Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button