Rahotanni
Wani Matashi Ya Siffanta Hancin Jaruma Rahama Da Na Mage..

Wani Matashi Mai Suna AmeeRul_Hayaat Yace Hancin Rahama Sadau Irin Na Mage Ne.
Matashin dai Yayi Tsokaci Ne Akan Hoton Da Jaruma Rahama Sadau Ta Wallafa A Daren Nan A Shafinta Na Twitter, Inda Yace ” Gaskiya Kinada Kyau, Amma Hancinki Irin Na Mage, Kuma Kinada Da Katon Baki”.

Sai Dai Kuma Tuni Matashin Yayi Istigifari Bayan Da Wani Yayi Masa Magana Akan Abin Da Yayi Bai Dace Ba, Inda Yarubuta Astagfirullah Sau Uku.
Amma Kuma Bai Bawa Jarumar Hakuri Ba. Abin Jira Agani Dai Shine Natakin Da Jaruma Rahama Sadau Zata Dauka Akan Wannan Matashi. Shin Zata Hakura Takyaleshi, Ko Kuwa Itama Zata Maida Masa Martani da Zazzafan Kalami?
