Rahotanni

Wani Mutum ya binne Jikansa Jariri da ransa a Bauchi.

Spread the love

Rundunar ‘Yan sandan Jihar Bauchi ta kama wani uba dan kimanin shekara 50 da ake zargin ya binne jikansa (jariri) a raye.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Bauchi DSP Ahmed Mohammed Wakil, ne ya shaida wa Manema Labari cewa mutumin da ta bayyana Bawada Audu ya aikata kisan bayan ‘Yarsa mai shekara 17 ta haifi Jariri.

Ƴ’Yan sandan sun ce an yi wa yarinyar fyade ne a watan Janairu, kuma ta samu ciki har ta haihu. Kuma ƴ’Yan sandan sun ce mahaifin yarinyar ya kashe jaririn ne saboda yana gudun abin kunya.

Ƴ’Yan sandan sun ce sun samu labarin ne daga wata ƙkungiyar kare hakkin dan Adam, da ba su bayyana sunanta ba inda kuma suka ƙkaddamar da samame a ranar 16 ga watan Satumba sukayi nasarar Kama Mai Laifin.

“Mahaifin ya amsa cewa shi ya karbi jaririn kamar da misalin ƙkarfe biyu na dare bayan ‘Yarsa ta haihu, ya tafi bayan gidansa ya binne shi da ransa,” a cewar ƴ’Yan sandan Bauchi.

Mahaifin kuma ya shaida wa ƴ’Yan sandan cewa dalilin kashe jikansa saboda ‘Yarsa ta kawo masa abin kunya shi ne ya sa ya halaka shi.

Ƴ’Yan sandan sun kuma ce bayan jin cewa an binne jaririn da ransa suka tono shi a inda aka binne shi bayan garzayawa da jaririn asibiti, likitoci suka tabbatar da jaririn ya rasu bayan an binne shi.

Yarinyar ta shaida wa ƴ’Yan sanda cewa wani mai suna Danjuma Malam Uba, ne ya yi mata ciki, wanda kuma yanzu ya tsallake.

Rundunar ƴ’Yan sandan Bauchi ta ce tana kan bincike domin kama shi don jin daga bakinsa kan zargin ciki da yarinyar ta ke zargin ya yi mata.

Ƴ’yan sandan sun ce suna tsare da mahaifin yarinyar da ake zargi ya kashe jikansa, kuma suna kan gudanar da bincike don tabbatar da gaskiyar al’amarin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button