Wani Mutumi A Katsina Ya Kulle Dansa A Keji Kamar Kare Har Tsawon Shekaru Hudu, Bayan Da Mahaifiyarsa Ta Rasu.
An ciyar da shi kamar kare a cikin lokacin har zuwa makon da ya gabata lokacin da SCI ta shiga tsakani kuma ta kai rahoto ga ‘yan sanda.
Wata kungiya mai zaman kanta, Save the Children International, ta ceto wani yaro dan shekara 16 da aka bayyana da suna Sadiqu Daura, wanda mahaifinsa, Salisu Umar Daura, ke tsare dashi cikin keji tsawon shekaru hudu, a gidansa da ke Daura, Jihar Katsina.
Kulle Sadik ta fara ne lokacin da ya rasa mahaifiyarsa shekaru shida da suka gabata.
Da yake yana da matsala a jiki, sai aka kai shi wurin kakarsa, wacce ita ma ta mutu ba da jimawa ba.
Daga baya aka dawo da Sadiqu gidan mahaifinsa kuma aka saka shi a cikin keji sakamakon halin da yake ciki.
An ciyar da shi kamar kare a cikin lokacin har zuwa makon da ya gabata lokacin da SCI ta shiga tsakani kuma ta kai rahoto ga ‘yan sanda.
A cewar wani jami’in SCI a Daura, Aminu Gambo, Salisu ya fadawa ‘yan sanda cewa ya yanke shawarar saka yaron ne a cikin kejin saboda babu sauran sarari a gareshi a cikin mai daki biyu wanda zai dauke dukkan iyalai 15 ciki har da sauran yaransa 12. .
“An tsare shi a ofishin‘ ‘yan sanda da ke Daura na yini guda sannan daga baya ya koma hedikwatar ‘yan sanda da ke Katsina sannan daga baya aka sake shi da sharadin ba zai kara mai da yaron ga irin wannan halin rashin mutuntaka ba.
“SCI na aiki don ganin yadda za ta saukar da Sadiku a karkashin shirinta na Samarwa da Karfafawa ga matasa don yin zabin da ya dace game da shirin lafiyarsu da ake aiwatarwa a jihohin Zamfara, Katsina da Gombe,” in ji shi.
Daga Sabiu Danmudi Alkanawi