Labarai
Wani Soja Mai Suna Kaftin Balare Tijjani Shine Yake Bawa Wadume Kariya.
Wani dan uwan Bala Hamisu (Wadume) ya ce sojoji karkashin Umurnin Kaftin Tijjani Balarabe sun kasance suna dan uwansa Hamisu Wadume.
Kawu Mohammed, dan asalin jihar Taraba ne, ya bayyana cewa Wadume yana jin daɗin kariyar ta sojoji, haka kuma sojoji sun kasance amintattu a gare shi a Taraba.
A cikin bayanin da ya gabatar ga ‘yan sanda ranar 29 ga watan Agusta, 2019, Muhammad ya ce dan uwan wadume Auwalu Bala ne ya ce yaje wata tashar watsa shirye-shirye ya karyata labarin ‘yan sanda kan batun satar dan sanda wanda ke fuskantar shari’a a Abuja.
A cewarsa daga baya Auwalu ya sanar da shi cewa ya tura a wata kungiyar masu watsa labarai da aka yi haya don yiwa hoton Wadume.