Tsaro

Wani Tubabban Dan Boko Haram Ne Ya Fadamin Wani Gwamnan Arewa Mai Ci Ne Kwamandan Boko Haram~ Mailafiya Ya Amsa Gayyatar DSS Yau.

Spread the love

Bugu da kari Mailafiya ya girmama gayyatar DSS, ya ce “idan na halaka, na halaka”

Dan takarar shugaban kasa na African Democratic Congress kuma tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Dokta Obadiah Mailafiya, a ranar Litinin, ya sake girmama gayyatar da Hukumar Kula da Harkokin Jiha (DSS) ta yi masa.

Mailafiya ya ce idan saboda ya yi magana game da halin da ‘yan kasa ke ciki na rashin tabbas, zai halaka, haka ma lamarin yake.

Ya ce “Ni ne muryar shahidai tsarkaka, kuma idan na halaka, na halaka”.

Wannan shi ne karo na uku da DSS ke gayyatar Mista Mailafiya kan kalaman da ya yi ta rediyo, game da Boko Haram.

Mailafiya ya yi zargin cewa tubabben dan Boko Haram ya fada masa cewa wani gwamnan arewa mai ci ne kwamanda na kungiyar ta’addan.

Da yake magana da manema labarai kafin ya shiga hedikwatar DSS da ke Jos, Mailafiya wanda ya iso da karfe 11:09, ya ce, “Ni ne muryar miliyoyin mutane marasa magana.

“Matasan Musulmi da Kirista duk sun dauke ni a matsayin muryarsu.”

“An kashe dubunnan mutane a kasar nan; a Borno, Yobe, Adamawa, Katsina, Zamfara, Niger, Birnin Gwari, Kudancin Kaduna, Benue, Plateau da sauran sassan kasarnan ”.

Ya ci gaba da cewa, “Ni muryar shahidai masu tsarki ne kuma idan na halaka, na halaka”.

Idan baku manta ba Babbar Kotun Jiha da ke zaune a Jos, a ranar Juma’ar da ta gabata ta sanya 29 ga Satumba, 2020, don yanke hukunci kan karar da Mailafiya ya shigar.

Tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin na kalubalantar gayyatar da ofishin sashin binciken manyan laifuka na DIG, Abuja ya yi masa.

Mailafiya yana rokon Kotu da ta bayyana cewa Ma’aikatar Tsaron Kasa (DSS) ita ce kadai doka wacce doka ta ba ta ikon magance aikata laifuka a kan Tsaron Cikin Najeriya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button