Siyasa

Wannan Cin Amanar ‘Yan Kasa Ne Da Jefa Da Kokarin Jefa Mutane Cikin Rikici Gwamnatin APC Takeyi, Inji PDP.

Spread the love

Jam’iyyar PDP ta Chaccaki Gwamnatin APC kan Farashin Fetir.

Ahmed T. Adam Bagas

Jam’iyyar PDP ta bayyana sabon farashin mai daga N145 zuwa N151 a kowace lita a matsayin Cin amanar ‘Yan Kasa da kokarin jefa mutanen kasar cikin rikici.

Jam’iyyar adawar a cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labaranta, Kola Ologbodiyan, ya fitar jiya Laraba ta ce tana mamakin dalilin da ya sa gwamnati da gangan take kokarin sanya rayukan ‘yan kasa da ke hulda da tattalin arziki cikin wahala a lokacin nan na cutar COVID-19 da tsadar kayan Abinci.

PDP ta ce, “Abin takaici ne yadda gwamnatin APC ta kara kudin kayayyakin masarufi a lokacin da shugabannin wasu kasashen ke ba da tallafi ga‘ yan kasa don rage radadin zaman gida lokacin cutar COVID-19. Yana da kyau mu gane cewa al’ummar mu ta lalace a karkashin APC.

“Bugu da kari, APC da gwamnatinta sun kasa ba da damar bude bincike kan zarge-zargen karin kudin man fetur da kuma tsarin bayar da tallafi na yaudara wanda tace tana bayarwa tace ta kashe sama da Naira tiriliyan 14 da suke ikirarin sun kashe.

“Tsoronmu shi ne APC tana tura‘ yan Najeriya bango tare da ayyukanta na nuna rashin tausayi da kyamar mutane, kuma gwamnati tayi taka-tsantsan da abinda takewa ‘yan kasa, kar taga son zaman lafiya da bin doka da oda na ‘yan Najeriya a matsayin alamar tsoro ne sai dai kokarin son zaman lafiya.

“Don haka jam’iyyarmu ta sake kira ga Majalisar Dokoki ta kasa don ceton al’umma ta hanyar kiran APC da gwamnatinta da su yi duk mai yiwuwa kafin su jefa al’ummarmu cikin rikici Inji Shi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button