Ɗan Wasan Everton Da Italiya Moise Kean, Mai Shekara 20 Yana Son Komawa Juventus.

Kasuwar ‘yan kwallo: Makomar Bellerin, Bale, Kean, Mendy, Ritchie, Luiz, Lacazette

Barcelona ta tuntubi Arsenal kan yiwuwar dauko dan wasan Sufaniya Hector Bellerin, mai shekara 25. (Sport – in Spanish)

Zakarun kwallon kafar Faransa Paris St-Germain suna son dauko Bellerin kuma sun tuntubi wakilansa. (Independent)

Real Madrid za ta amince ta biya rabin albashin Gareth Bale domin ta saukaka wa dan wasan na Wales mai shekara 31 ya bar kungiyar. (Telegraph – subscription required)

Dan wasan Everton da Italiya Moise Kean, mai shekara 20, yana son komawa Juventus, inda daga can ne kungiyar ta dauko shi a 2019. (Calciomercato – in Italian)

Rennes ta tabbatar cewa tana tattaunawa da Chelsea a kan yiwuwar karbo golan Senegal Edouard Mendy, mai shekara 28. (Goal)

Kocin Ingila Gareth Southgate zai yi tattaunawa ta ƙeƙe-da-ƙeƙe da dan wasan tsakiyar Manchester City Phil Foden, mai shekara 20, da dan wasan Manchester United Mason Greenwood, mai shekara 18, bayan an kori ‘yan wasan biyu gida saboda sun karya dokar annobar korona. (Mail)

Bournemouth tana son sake dauko dan wasan Scotland Matt Richie daga Newcastle sai dai har yanzu ba ta cika sharudan dauko shi ba. (Newcastle Chronicle)

Dan wasan Arsenal da Brazil David Luiz, mai shekara 33, zai iya rasa wasan wata daya a kakar bana sakamakon matsanancin ciwon wuyan da yake fama da shi. (Telegraph – subscription required)

Aston Villa tana son dauko dan wasan Bournemouth da Norway Joshua King, amma dan wasan mai shekara 28 ya fi son tafiya Manchester United bayan an gaza cimma yarjejeniyar tafiyarsa Old Trafford lokacin musayar ‘yan kwallo a watan Janairu. (Athletic – subscription required)

Dan wasan Arsenal da FaransaAlexandre Lacazette, mai shekara 29, yana neman karin bayani kan rawar da zai taka a kungiyar sakamakon rade radin da ake yi cewa za a sayar da shi da bazara. (ESPN)

Aston Villa ta ware sama da £15m inda ta taya golan Arsenal dan kasar Argentina Emiliano Martinez, mai shekara 28, bayan an ki karbar tayinta na farko. (Goal)

Manchester United ta kammala sayen matashin dan wasa mai shekara 16 Alejandro Garnacho daga Atletico Madrid. A cikin makon nan ne dan wasan zai isa Old Trafford daga Sufaniya, kodayake zai killa kansa tsawon mako biyu. (Manchester Evening News).

Daga Amir Sufi

Leave a Reply

Your email address will not be published.