Ahmad Musa Ya buga wasansa na farko a Kano Pillars.

Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles kuma sabon dan wasan Kano Pillars Ahmad Musa, ya fafata wasansa na farko a kungiyar a wasan sada zumunci da suka buga da Dabo Babes a filin Bukavu Barrack da sukai nasara da ci 5 da 2.

Musa ya dai fafata zagayen farko na wasan, wanda a lokacin Pillars ke kan gaba da ci biyu babu ko daya.

Kafin daga bisani mai horar da kungiyar Ibrahim A. Musa ya sau yashi da wani dan wasan a zagaye na biyu na wasan.

Haka zalika Ibrahim A. Musa ya bayyana sun gudanarda wasanne a shirye-shiryen da suke na da wowa wasannin gasar Firimiya ta Kasa da za’a dawo a ranar Tara ga watan Mayu mai kamawa.

Rahoto Ahmad Hamisu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *