Aston Villa Ta Amince Ya Sayi Watkins Kan £28m Daga Brentford.

Aston Villa ta kusa kammala sayen dan wasan Brentford Ollie Watkins bayan ta amince ta biya £28m abin da zai kara kudin zuwa £33m idan aka hada da alawus.

Villa ta yi gaggawar taya dan wasan mai shekara 24 bayan ta gaza sayen Callum Wilson daga Bournemouth.

Dan wasan na Ingila ya gwammace ya tafi Newcastle United a kan £20m.

Watkins yana cikin ‘yan wasan da suka yi bajinta a Brentford a kakar wasan da ta wuce, inda ya zura kwallo 26.

Kocin Villa Dean Smith ya ce zai dage wajen ganin ya inganta bangaren masu kai hari na kungiyar.

Daga Amir Sufi

Leave a Reply

Your email address will not be published.