Barcelona na shirye shiryen siyan ɗan Najeriya mai takawa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Leicester City leda.


A cewar rahotanni daga kasar Andalus, ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta La liga, Barcelona zata yi yunƙurin siyan ɗan wasan Super Eagles mai suna Wilfred Ndidi daga kungiyar Leicester City.

Kafofin watsa labarai na ƙasar Andalus, El Gol Digital sun ruwaito cewa shahararriyar ƙungiyar ta Kataloniya sun gano Ndidi a matsayin wanda zai iya maye gurbin Sergio Busquet wanda, wanda tsufa ke cimma, wanda hakan zai iya barin Basquet yayi gaba a wannan bazarar.

Ndidi yana ɗaya daga cikin ƴan wasa da tauraron su ke haskakawa a ƙungiyar Liecester City a wannan kakar, inda ya buga wasanni 28, ya ci ƙwallo 1, sannan kuma ya taimaka aka zura ƙwallaye 3.

An kuma alaƙanta ɗan wasan da komawa Real Madrid, PSG, da kuma Manchester United amma Barcelona a shirye take ta gabatar da tayin da baza’a ce a’a ba domin ganin sun ɗauki ɗan wasan.

Yarjejeniyar Ndidi da Leicester ta yanzu zata ƙare ne a 2024 kuma darajarshi a cikin kasuwar cinikayya zatai wajen Yuro miliyan 60 .

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *