Barcelona Ta gaza samun damar hawa teburin LaLiga

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona tayi rashin nasara akwan tan wasan gasar La Liga ta kasar Andalus bayan rashin nasara da tai da ci daya da biyu a hannun Granada a yammacin yau Alhamis.

Tunda fari Barcelona ce ta fara zura kwallon farko ta hannun dan wasa Messi, kafin daga bisani a farke kwallon da ya zura a wasan da aka tashi 2-1.

Sakamakon ya nuna Barcelona ta taza samun damar hawa Teburin gasar, inda yanzu haka ta ke mataki na uku da maki 71, inda Real Madrid ta ke ta biyu da maki 71 sai kuma Athletico Madrid da ta ke ta farko da maki 73 a wasanni 33 da aka buga.

Rahoto: Ahmad Hamisu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *