Buffon ya zargi Ronaldo da gaza kokari a Juventus

Mai tsaran ragar Juventus Gianluigi Buffon, ya ce gaza kokarin kungiyar ya biyo bayan rashin kokarin dan wasan Cristiano Ronaldo a kakar wasannin da muke ciki.

Mai shekaru 43 ya kuma kara da cewa dan wasa Ronaldo kowa ya san na da hatsarin gaske da kuma taka rawagar gani a ko wanne ya nayi ya tsinci kanshi.

Juventus kawo yanzu dai na burin kasan cewa cikin kungiyoyin da zasu wakilci kasar Italiya a gasar kofin zakarun turai na Champions League a kakar wasanni mai zuwa, inda ta ke a mataki na biyar maki daya tsakaninta da Napoli da ke a mataki na hudu.

Koda a gasar kofin zakarun turai da muke ciki Juventus ta gaza doke FC Porto.

“Matuka inada kyakykywar alaka da dan wasa Ronaldo, domin kuwa nasanshi matuka da hakan ya sa muke da abota sosai,” a cewar Buffon ya yin ganawarsa da beIN Sports.

Ya kuma kara da cewa ba abun mamaki bane gaza kokari da sauran ‘yan wasan kungiyar sukai, amma gudunmawar Ronaldo shikadai zata fi ta sauran ‘yan wasa da dama a kungiyar.

Haka zalika ya ce na bawa Juventus duk abun da ya ke da akwai domin samun nasarar kungiyar da a yanzu kowa ya ga irin halin da tawagar ke ciki na rashin tabuka abin azo agani.

Rahoto: Ahmad Hamisu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *