Chelsea Ta Lashe Kofin Zakarun Nahiyar Turai Na Bana

Ƙungiyar ƙwallon ƙafar Chelsea ta ƙasar Ingila ta lashe kofin zakarun nahiyar turai na bana bayan data doge abokiyar hamayyarta Manchester City da ci ɗaya mai ban haushi ta hannun ɗan wasanta Kai Harvertz daya zuwa ƙwallonsa a raga a minti na 42 da fara wasan.

Kungiyar ta samu wannan nasarar ne ƙarƙashin mai horar da ita Thomas Tuchel bayan kwanaki 156 da sallamarsa daga tsohuwar ƙungiyarsa ta PSG.

Sannan wannan kofin shine na biyu da ƙungiyar ta lashe a tarihi tun shekarar 2012

Daga Mutawakkil Gambo Doko

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *