Daga Ƙarshe: Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Inter Milan ta samu nasarar ɗaukan kofin gasar Serie A

A karon farko cikin shekara goma sha ɗaya bayan tayi canjaras da Atlanta da take a matsayin na biyu da ita da Sassuolo, ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Inter Milan sune sukayi nasarar lashe gasar Serie A.

Tunda fari dai, Inter ta bayar da maki goma sha uku ne a saman jadawalin buga gasar Serie A ɗin ne, tun bayan nasarar data samu a ranar Asabar yayin da ya rage saura wasanni huɗu a kammala gasar.

Maki ɗaya ne ya shiga tsakanin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Inter da Juventus da ta lashe gasar a shekarar data gabata, sai dai a wannan karon Antonio Conte ya bai wa Juventus zunzurutun maki har guda tara ne a shekara ta biyu da kasancewar sa a matsayin mai horar da kungiyar ta Inter Milan.

Wannan shine kofi na farko da Inter Milan tayi nasarar lashewa tun lokacin da shahararren mai horarwar nan wato José Mourinho ya lashe, wato lokacin daya ci kofi uku rigis da suka haɗa da gasar Serie A da Champions League a shekarar dubu biyu da goma.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *