Dan wasan Kai Havertz ya zura kwallo biyu a wasan Chelsea da Fulham

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta cigaba da rike mataki na hudu a gasar Firimiya bayan dan wasa Kai Havertz ya zura kwallo biyu a wasan da suka fafata da Fulham a yau Asabar sukai nasara da ci 2-0.

Jagoran kungiyar Thomas Tuchel dai na shirin tunkarar buga wasa da Real Madrid a ranar Laraba a gasar kofin zakarun turai a filin wasa na Stamford Bridge.

Havertz ya fara zura kwallon farko tun a zagayen farko na wasan da hakan ya sa Chelsea ta bawa West Ham ta zarar maki shida.

Sai dai West Ham zata bu’ga wasa a ranar Litinin da Burnley.

Nasarar zura kwallo da Havertz ya yi ya bashi damar zura jumullar kwallo takwas a kakar wasannin da muke ciki ma Chelsea, sai dai kamuwa da cutar coronavirus da dan wasan ya yi ya hanashi damar buga wasanni akai-akai

Chelsea dai karsashinta ya da wo tun bayan sallamar tsohon gwarzan dan wasanta Frank Lampard da ta maye gurbinsa da Tuchel a wasan Janairun da ya gabata.

Tuchel wanda tsohon mai horar da Paris Saint-Germain ne ya karbi kungiyar a mataki na tara, inda a yanzu suke a matai na hudu da kawo yanzu ya yi nasar kaiwa matakin wasan karshe a gasar FA Cup dq zasu fafata da Leicester a watan Mayun da muke ciki.

Haka zalika Chelsea zata karbi bakuncin Real Madrid a wasan zagaye na biyu na matakin kusa da karshe a gasar kofin zakarun turai a ranar Laraba, bayan tunda fari a wasan farko an tashi 1 da 1 tsakanin kungiyoyin biyun.

Rahoto: Ahmad Hamisu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *