Iheanacho ya kuma lashe kyautar ɗan wasa mafi hazaƙa ta kasar Ingila.

Dan wasan gaban Leicester City Kelechi Iheanacho, ya lashe kyautar gwarzan dan wasan wata na Gasar Firimiya ta kasar Ingila.

Dan wasan dai shine ya lashe kyautar gwarzan watan Maris kafin ya sa ke lashe ta watan Afrilu da ta gabata.

Sakamakon rawar da dan wasan ya taka ya baiwa mai horarda tawagar BrendanRogers fafata wasanni biyar inda tayi nasara a wasanni biyu, kunnan doki a wasa daya da kuma rashin nasara a wasanni biyu da hakan ya bata nasarar samaun maki bakwai maimakon 15 da ya kamata ta samu.

Iheanacho ya zura kwallaye hudu da kuma taimakawa aka zura kwallo biyu a wasannin da ya fafata.

Mai shekarau 24 Iheanacho ya yi nasarar doke ‘yan wasa irinsu Trent Alexander-Arnold na Liverpool da dan wasan Leeds UnitedStuart Dallas sai Mason Greenwood na Manchester United da Jesse Lingard na West Ham da ɗan wasan West Brom Matheus Pereira da ɗan wasa Allan Saint-Maximin na Newcastle United da kuma dan wasa Chris Wood na Burnley.

Rahoto: Ahmad Hamisu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *