Ina fatan Iwobi ya dawo tawagar Arsenal-Aubameyeng

Dan wasan gaba na Arsenal Pierre-Emerick Aubameyang, ya ce yana da burin ya ga dan wasan Super Eagles , ta Najeriya Alex Iwobi, ya sake fafata wasa a kungiyar.

Iwobi ya bar Arsenal a shekara ta 2019, bayan komawa Everton akan kudi Euro Miliyan 30.Kafin barin sa Arsenal a lokacin Iwobi ya zura kwallaye 15 a wasanni 149 da ya fafata.

Ina da burin naga na sake fafata wasa da Alex Iwobi, sakamakon muna da fahimtar juna dashi sosai ina mafarkin hakan ya faru,” cewar Aubameyang.

Rahoto: Ahmad Hamisu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *