Karan batta tsakanin Real Madrid da Chelsea a gasar kofin zakarun turai.

A yau Talata za’a fafata wasan kusa da karshe na kofin zakarun turai Champions League tsakanin Real Madrid da ga kasar Andalus, da kuma Chelsea da ga kasar Ingila, wasan da zai gudana da misalin karfe takwas na dare 8:00.

To sai dai a tsakanin wadannan kungiyoyi a wasanni uku baya da suka fafata, Real Madrid tayi nasara a wasanni biyu, sai kuma Chelsea tayi nasara wasa daya.

Inda a ranar 6 ga watan 8 shekara ta 1998 an fafata wasa tsakaninsu a gasar kofin UEFA Super Chelsea nasara tayi akan Madrid da ci daya babu ko daya.

Ya yinda a ranar 9 ga watan 8 na shekara ta 2013 a gasar International Champions Cup Madrid tayi nasara akan Chelsea da ci 3 da 1.

Sai kuma wasan baya-bayannan da ya gudana tsakaninsu a dai gasar ta international Champions, Chelsea rashin nasara tayi da ci 2 da 3 akan Madrid wasan da ya gudana a ranar 12 ga watan 7 na shekara ta 2016.

Shin mene hasashenku a wasan?

Rahoto: Ahmad Hamisu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *