Real Madrid ka iya doke Chelsea a wasan Kofin zakarun turai a Laraba – Sahin

Dan wasan tsakiyar kasar Turkiyya Nuri Sahin, ya bayyana kungiyar Real Madrid rid ka iya doke Chelsea a wasan kusa da karshe na kofin zakarun turai wasa zagaye na biyu da zai gudana a gobe Laraba.

Wasan farko dai an tashi wasa daya da daya 1-1 tsakanin kungiyoyi biyun.

Sahin, Wanda ya taba bugawa Borussia Dortmund wasa a shekara ta 2013,ya kuma fafatawa Real wasa a shekara ta 2011/212.

“Ina tunanin cewa kowa yasan a yanzu yadda wasan ya ke kasan cewa, musamman ganin yadda duka kungiyoyin ke buga wasa mai kyai da kuma kayatarwa,”

Haka zalika ya ce koda kungiya kamar ta Chelsea da mai horarwa Thomas Tuchel ke jagoranta babu shakka suna wasa mai kyau, sai dai ya fi bawa tawagar da Zinedine Zidane ke jagoranta nasara sakamakon kwarewa da ya ke da ita a matsayin mai horarwa da ya jagoranci kungiyar lashe gasar har karo uku a baya.

Rahoto: Ahmad Hamisu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *