Victor Valdes na shirin sake da wowa Barcelona.

Tsohon mai tsaran ragar kungiyar kwallon kafa ta Barcelona Victor Valdes na shirin sake da wowa filin wasan tawagar na Camp Nou.

Valdes wanda ka iya da wowa domin aikin horarda Barcelona wanda sabon shugaban kungiyar Joan Laporta ke shirin yin aiki dashi.

Valdes tsohon dan wasan Manchester United da a yanzu ya ke horar da kungiyar La Masia.

Mai shekaru 39 ya lashe gasanni daban-daban kafin ya bar kungiyar da ke birnin Catalan a shekara ta 2014.

Kafin da ga bisani ya bugawa kungiyoyin Standard Liege da kuma Middlesbrough.

Valdes ya lashe gasar La Liga a shekarun 2004, 2005 , 2008, 2009 , 2010 da kuma 2012.

Haka zalika ya lashe Copa del Rey sau biyu, gasar Supercopa de España guda shida, gasar kofin zakarun turai guda uku da kuma gasar UEFA Super Cup guda biyu da kuma gasar FIFA Club World Cup itama guda biyu.

Ya yinda ya kuma lashe gasar kofin duniya da kasar ta Andalus (Spain) a shekara ta 2010 da kuma gasarUEFA European Championship a shekara ta 2012.

Rahoto: Hamisu Ahmad

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *