Wasanni

Yariman Saudiyya Mai Jiran Gado Ya Isa Kasar Qatar Domin Kallon Buga Gasar Cin Kofin Duniya

Spread the love

Kafofin yada labaran kasar Saudiyya sun ruwaito cewa, yarima mai jiran gadon sarautar Saudiyya da tawagar ministocin kasar sun isa makwabciyar kasar Qatar da safiyar Lahadi domin halartar bikin bude gasar cin kofin duniya.

Kamfanin dillancin labaran Saudiyya ya bayyana cewa, Mohammed bin Salman ya samu rakiyar ministocin makamashi, cikin gida, harkokin waje, kasuwanci da zuba jari da kuma manyan jami’ai da suka hada da mai ba shi shawara kan harkokin tsaro na kasa da kuma shugaban rundunar tsaron kasar.

Yarima Mohammed, mai shekaru 37 a duniya mai mulkin Saudiyya, ya kitsa killace kasar Qatar tun a watan Yunin 2017, a watan da ya zama na farko a kan karagar mulki.

Saudiya, Hadaddiyar Daular Larabawa, Bahrain da Masar sun yanke hulda da Doha bisa zarginta da goyon bayan masu tsattsauran ra’ayi da kuma kusanci da babbar abokiyar hamayyarta Iran – zargin da Doha ta musanta.

Kasashen hudu sun amince da dage takunkumin a taron kungiyar hadin kan kasashen yankin Gulf a watan Janairun 2021 a birnin Al-Ula na kasar Saudiyya.

Yarima Mohammed ya je Qatar ne a watan Disambar bara, tare da Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani, sun ziyarci filin wasa na Lusail, wanda zai kasance wurin da za a buga wasan karshe na gasar cin kofin duniya ta bana.

Ba a dai bayyana tsawon lokacin da Yarima Mohammed, wanda a kwanan baya ya kammala rangadin kasashen Asiya, ya yi niyyar ci gaba da zama a Qatar ba.

A ranar Talata ne kungiyar kwallon kafa ta Saudiyya Green Falcons za ta buga wasanta na farko da Argentina.

AFP

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button