Kunne Ya Girmi Kaka

WASU ABUBUWAN TARIHI DA SUKA FARU A GARIN ZUNGERU NA JIHAR NIGER

Spread the love

1-A wannan wani gida ne a garin Zungure na jihar Niger wanda a cikinsa ne baturan mulkin mallakar nan mai suna Frederick Lugard a ranar 1 Janairu 1914 ya saka hannu a daftarin takardunsu da zasu haɗe kudanci da arewacin Najeriya a matsayin ƙasa ɗaya (Amalgamation of Southern and Northern protectorate).

2- Sannan garin Zungeru na jihar Niger shine farkon babban birnin lardin arewacin Najeriya daga shekarar 1902 zuwa 1912.

3- Bugu da ƙari, an haifi shahararrun ƴan siyasa a garin Zungeru na jihar Niger. Kamar irinsu :

1- Dr. Benjamin Nmandi Azikiwe wanda aka haifeshi a ranar 16 Nov 1904 a garin na Zungeru sannan ya mutu a ranar 11 May 1966. A garin ne ya koyi harshen Hausa wanda daga baya suka koma Onitsha shi da gwoggonsa da kakarsa wanda dalilin hakan ne yasa ya koyi yaren Iyamuranci (Igbo) a garin, sannan daga baya ya zauna a jihar Legas nan ma ya koyi yaren Yarabanci . Wato yana dai shine shugaban ƙasar dayake jin manyan yarukan Najeriya babu gargada guda uku (Hausa, Igbo, Yaruba ).

  • Dr Nmandi Azikiwe shine shugaban Najeriya na farko daga shekarar 1963 zuwa 1966(Bayan ƙasar ta koma ta farkin jamhuriya)

2- Sannan a garin Zungeru na jihar Niger aka haifi Sanata David Mark a watan Aprill 1948.

  • Sanata David Mark ya rike muƙamin ministan sadarwa na ƙasa

*Sanata David Mark yayi gwamnan jihar Niger na soji daga shekarar 1984 zuwa 1986.

*Sanata David Mark ya riƙe muƙamin shugaban majalissar dattawan Najeriya daga watan June 2007 zuwa shekarar 2015. Wanda sanata Bakola Saraki ya maye gurbinsa.

3- Chukwuemeka Ojukwu shima a garin Zungeru na jihar Niger aka hafeshi a shekarar 1933. Sannan ya rike gwamnan lardin gabashin Najeriya a shekarar 1966.

  • A shekarar 1967 zuwa 1970 yayi fafutukar kafa haramtaciyar jamhuriyar Biafra wacce zata ɓalle daga tarayyar Najeriya. Ya mutu a ranar 26 Nov 2011 a ƙasar Burtaniyya bayan gajeriyar jinya yana da shekaru 78 a duniya.

Daga Mutawakkil Gambo Doko

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button