Tsaro

Wasu da ake zargin Sojoji ne Sun Bude Wuta kan Mutane a Maiduguri.

Spread the love

Wasu ‘yan bindiga sanye da kayan sojoji sun bude wuta a kan wasu gungun mutane, lamarin ya farune a Baga Road a cikin Maiduguri, ta Jihar Barno, Arewa maso Gabashin Najeriya.

Wannan mummunan al’amari ya farune Jiya talata, wasu ‘yan garin sunce, lamarin na da nasaba da kisan wani sojan Najeriya da wasu fusatattun mutane suka yi a wani Otal (Barka da Zuwa).

Barka da Zuwa, dai wajen Shakatawa ne na Sojoji da Wajen boyewa na masu aikata Laifuka a Maiduguri.

Rahoto yace a ranar Asabar ne wani Soja ya Harbe wani Matashi a Barka da Zuwa, ‘Yan Uwan Matashin kuma suka kashe Sojan, An zargi ‘yan Uwan Sojan da aka Kashe ne suka Shigo Ramuwar Gayya.

Lamarin wanda ya faru da misalin 8 na dare ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane biyu, yayin da wasu uku ke dauke da raunuka suna amsar magani.

Wannan jaridar ta tattaro cewa maharan da ake zargin sojoji ne a kan ramuwar gayya kan mutuwar abokin aikinsu sun yi ta harbe Harbe, tare da yin garkuwa da mutane hudu.

An gano biyu daga cikin mutanen da aka sace sun mutu a kusa da Shagari Lokos, yayin da aka harbe sauran biyun a ƙkafafunsu.

Wasu rahotanni sun ce wasu mazauna yankin sun taru a yankin a yau Laraba, da rana kuma suna zanga-zangar nuna adawa da lamarin.

Wata majiya ta shaida wa wakilinmu cewa Barka da Zuwa ya zama mafaka ga masu aikata laifuka da sojoji.

Gwamnatin Jihar Borno a cikin 2018 ta ayyana a kalla otal-otal 47 a cikin Maiduguri, babban birnin jihar, wanda aka bayyana a matsayin “gidajen giya mara izini,” kuma Za’a Rushesu.

Kaka Shehu Lawan, Babban Lauyan Gwamnati kuma Kwamishinan Shari’a ya ambaci barazanar tsaro da Habaka lalata a tsakanin matasa kamar yadda wasu manyan dalilan da gwamnati ta sanya alama ga gine-ginen.

Lawan ya ruwaito daga Jaridar Premium Times a shekarar 2019 yana cewa kusan gidajen karuwai 20, gidajen giya, da otal otal ba bisa ka’ida ba saboda karya dokokin jihar da suka kullesu a shekarar 2018.

Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button