Uncategorized

kayan masarufi sunyi tashin gauron zabi

Idan APC da gaske take tanaso tasake darewa karagar mulki a 2023 ya kamata tadauki matakin gaggawa wajen samawa talaka kyakkyawan yanayin da zeyi rayuwa cikin sauqi.

Tun daga 2015 bayan APC ta karbi mulki daga hannun PDP cikin dan qanqanin lokaci komai ya ninka kudinsa, kama daga kayan larurar rayuwa har zuwa kayan morewa rayuwa.

Shinkafa ‘yar kura me kyau awancan lokacin mudu 1 # 300 kacal ake sayanta, amma a yau se ka sayeta #900 #1000 haka masara # 180#160 yau masara ta koma #450. #400 Dede da silifas yau silifas #300 ake saidashi alhali a #130 da APC suka taddashi.

Shugaba Buhari ya kamata tallafin da PDP ke baiwa talaka wanda da zuwanka kai da talaka ke tsammanin sauqi gurinka kaqi bawa talaka tun daga tallafin FETIR TAKI DALA KUJERUN HAJJI dama na gudanar da makarantun jami’oi ya kamata kasani talaka ke wahala.

Haka ma HARAJI daka zugawa kamfaninnika da COSTORM DUTY da kuka zambadawa kudi duk akan talaka yake qarewa, kuma idan da alqawari idan kowa yaqi talaka kai be kamata kaqishi ba, sabida kaine shugaban da yafi kowane shugaba a Najeriya amfanar talaka.

Banki haraji waya haraji, ya kukeso talaka yayi?

Inde da gaske kuke kunayi dan talaka ne to ya zama wajibi kukafa kwamiti asamo hanyar da talaka ze samu sauqi cikin gaggawa tun kafin wankin hula yakaiku dare, inko ba haka ba to babu shakka komawarku mulki a 2023 mafarki kuke.

Yadda talaka beji dadi a mulkin ku ba na tabbata duk talaka me hankali baze yadda yasake zabar ku ba sabida kowa ya yadda ana shan wahala aqasar nan.

Talaka na cikin halin ni ‘yasu, dan haka shawara ya rage ga me shiga rijiya, kuna ga kamar babu yadda talaka ya iya daku, amma Allah ba zai bar zalinci ya dore ba.

Daga Malama Aisha Golden.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button