Siyasa

Wasu gwamnoni sunfi ganin Indomie da mutunci fiye da rayukan mutanensu, in ji Shehu Sani.

Spread the love

Shehu Sani, wani tsohon dan majalisar dattijai, ya ce wasu gwamnoni sun fi ganin Indomie da muhimmanci fiye da rayukan mutane.

A wani abin da ya zama martani ne ga binciken gida-gida kan wawure shagunan da aka yi ajiyar kayan abinci a fadin kasar, Sani ya caccaki gwamnonin.

An yashe gidajen ajiya a duk fadin kasar cikin tashin hankalin da ya biyo bayan rikicin #EndSARS wanda ya kwashe kwanaki 13.

Abubuwa kamar su shinkafa, sukari, gishiri, garri, taliya, spaghetti duk an wawashe su.

A cikin wasu faya-fayan bidiyon da tuni suka fara yaduwa, da yawa daga cikin wadanda suka wawure dukiyar sun zargi gwamnatin jihar da ajiye kayan tallafin Covi-19.

Wasu gwamnoni sun ba da umarnin a bi gida-gida don kwato kayayyakin da aka wawushe.

Ahmadu Fintiri, gwamnan Adamawa, har ma ya yi barazanar rusa duk wani gini da aka samu kayan sata.

A wani sakon da ya wallafa a Twitter ranar Asabar, Sani ya ce: “Ga Gwamnoni; Indomie shine Zinare kuma rayuwar ɗan adam tagulla ce. ”

Sanarwar ta jawo maganganu, inda da yawa suka yarda da sanatan cewa wasu ‘yan siyasa basa ganin kimar rayuka.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button