Rahotanni
Wasu kungiyoyi a Arewa za su maka Shugaba Buhari a Kotu saboda kin sauya Shuwagabannin tsaron kasarnan
Gamayyar kungiyoyin Arewa na CNG sun bayyana cewa zasu maka shugaban kasa, Muhammadu Buhari a kotu saboda kin sauke shuwagabannin tsaro da yayi.
Yan Najeriya da dama na kira da a sauke shuwagabannin tsaro saboda zarginsu da rashin aikata abin a zo a gani. Saidai kakakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya sha kare shugaban kasar akan wannan lamari.
Kakakin CNG Abdulaziz Sulaiman ya bayyana cewa, a zamanin wadannan shuwagabannin tsaro matsalar tsaro a Arewa ta kara tabarbarewa. Yace dan haka akwai ka’idojin aiki da ya kamata abi wajan sauke wadannan shuwagabannin tsaro kuma dukansu sun cika wadannan ka’idoji dan hakane ma zasu je Kotu.
Daga Comr. Yaseer Alhassan Gombe.