Wasu kungiyoyi a jihohi 21 za su maka El-Rufa’i a kotu saboda ya ki yarda ya tsaya takarar shugaban Kasa
Kungiyar Nassiriya a cikin jihohi 21 na tarayyar kasar nan ta lashi takobin mara baya ga kudurin ta na neman Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’i zuwa takarar shugaban kasa a 2023.
Da yake zantawa da manema labarai a Kaduna, Shugaban kungiyar Nassiriya na kasa kuma Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na shiyyar Arewa maso Yamma, Dakta Garkuwa Ibrahim Babuga, ya ce tuni shirye-shirye sun yi nisa don kai El-Rufa’i zuwa kotu kan nacewarsa na kin sha’awar tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.
Babuga ya ce ba su da wani zabi da ya wuce su tunkari kotu saboda sun yi magana da gwamnan kan batun amma ya ki amincewa da bukatarsu.
“A shirye muke mu tafi zuwa Kotun Koli,” in ji shi.
“Mun kuma sadu da iyayensa da danginsa amma ba mu samu nasara ba. Dole ne mu je kotu. Najeriya ta El-Rufa’i ce a 2023. El-Rufa’i ya dace ya zama Shugaban kasa bisa la’akari da nasarorin da ya samu.
“Mutane da yawa suna kwadayin Shugabancin El-Rufa’i. Ba dole ba ne in cika ƙaho, duk kun ga nasarorin ci gaban sa a cikin FCT da kuma cikin jihar Kaduna. Shi ne mafi kyawun mutum ga Villa a 2023.
“Mu ci gaba da kasancewa masu biyayya da goyon baya ga Shugaba Buhari don kammala wa’adinsa. Amma El-Rufa’i a matsayin Shugaba kuma magajin Buhari zai kara hada kan Najeriya.
“Muna kira ga dattawan mu a Arewa, don Allah ku manta banbancin jam’iyya, ya kamata mu hada karfi wuri guda mu zagaya El-Rufa’i domin ya yi takara ya kuma ci shugaban kasa.
“Duk da cewa bai amsa kiran mu ba, za mu garzaya kotu domin tilasta wa El-Rufa’i ya tsaya takarar neman lamba ta daya a Najeriya.
“A ranar 2 ga Nuwamba, 2020 za mu je Kotun 13 a nan Kaduna. Lauyanmu Barista El-Zubair ne, ”inji shi.
Game da ikirarin da gwamna El-Rufai ya yi a kafafen yada labarai cewa yana goyon bayan wani shugaban kasa daga kudu ya zo 2023, shugaban kungiyar Nassiriya Organization ya ce wannan ra’ayin El-Rufai ne a wannan lokacin.
“Ra’ayinsa ne. Abin da kawai muke nema yanzu shi ne mu jawo shi cikin tseren. El-Rufa’i zai kasance mafi kyawun Shugaban Najeriya a 2023 da yardar Allah, ”inji shi.