Labarai

Wasu Ma’aikatan Gwamnati Sun Karbi Naira Miliyan 207 Lokacin Da Suka Tafi Barzahu.

Spread the love

Gwamnati Jihar Neja ta Gano Matattun Ma’aikata Har Guda 333, Suna karbar Albashi a Jihar.

Gwamnatin Jihar Neja karkashin Jagorancin Gwamna Abubakar Sani Bello, Ta gano Ma’aikatan Gwamnatin Jihar da Suka Rasu Sun Karbar Albashi har na Tsawon Shekaru Biyu, Mamatan Sun Karbu Albashi da yakai Naira miliyan 207 a bayan suna barzahu.

Kusan mako guda bayan gwamnatin jihar Neja ta sanar da korar wasu Ma’aikatan Gwamnati 80; gwamnatin jihar, har Ila yau ta gano cewa akwai matattun ma’aikatan gwamnati 333 na ci gaba da karbar albashi a jihar.

Wadannan matattun ma’aikatan da aka tabbatar sun mutu sun kasance cikin jerin albashin ma’aikatan jihar na shekaru biyu da suka gabata.

Kwamishinan Ayyuka, Injiniya Ibrahim Mohammed Panti wanda shi ne Shugaban Kwamitin Tantance ma’aikata a Jihar, ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai a Minna.

Ya kuma bayyana cewa an gano Naira miliyan 207 da aka biya a matsayin albashi ga wadannan matattun ma’aikatan jihar a cikin wadannan shekaru biyu.

“Daga cikin wadanda ake ikirarin cewa ma’aikatan gwamnati ne 27,000 ne a kan albashin gwamnatin jihar, 15,907 daga cikin su ne aka gano su ne ainihin ma’aikatan mu kawo yanzu Inji shi.

“Akwai ma’aikata 3,923 daga ma’aikatu daban-daban wadanda har yanzu tantancewar bata kawo kansuba.

“A cikin shekaru biyu da suka gabata, matattun ma’aikatan gwamnati 333 wadanda aka tabbatar da cewa sun mutu suna ci gaba da karbar albashi a jihar.”

Panti ya bayyana cewa aikin tantancewar wanda ke gudana ya kasance yana bayyana ayoyi masu ban mamaki yana mai jaddada cewa kwamitin ta kuduri aniyar bankado duk wadanda suka kwashe dukiyar gwamnati.

Ya kuma bayyana cewa Ma’aikatan Gwamnati 1,029 wadanda sunayen su ke cikin jerin masu daukar albashi daga gwamnati amma har yanzu ba su bayyana don a tantance su ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button