Wasu Mafarautan Sun Gwammace Su Rasa Uwayensu Fiye Da Karnukan Su A Cewa Mafarauci Ado Muhammad Maiduna Kano.
Wasu mafarautan sun gwammace su rasa uwayensu fiye da karnukan su, a cewar wani ma farauci, dan asalin jihar Kano, Ado Muhammad Maiduna.
Maiduna ya bayyana hakan ne, A yayin da, ‘yan kungiyar sa kai dake Unguwa Uku a karamar hukumar Tarauni (vigilante) ta ceci wani karen sa daga hannun wasu barayi.
A cewarsa, “Gaskiyar magana ba Unguwa Uku kawai ba, a duk duniya babu wani abu da mafarauci ya tsana fiye da satar karan sa, domin wani ya fi son mutuwar mahaifiyarsa da ya rasa karan sa. Inji Ado Maiduna.
Hakanan ya bayyana cewa, “kasan cewar Yanzu A na cikin yanayi da karnuka suke da daraja domin kuwa karnuka su kan kai kimanin Naira N20,000 ko kuma N30,000.
“Amma abun takaici sai yaro ya sace ma kare, ya je ya siyar dashi da kudin da baiwuce Naira N3,000 ko N5,000. Inji shi
Shima A ta bakin shugaban kungiyar ‘yan sa kai dake Unguwa uku Dauda Isma’il, ya bayyana cewa sun cafke wadanda a ke zargi mai suna Ciyalle da kuma Abba – da satar karnuka har guda Uku hadi da wani kare mallakar wani soja.
A cewarsa, sun aike da wadanda a ke zargi zuwa Ofishin hukumar ‘yan sanda mafi kusa.
Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe