Tsaro
Wasu Mahara Dauke Da Makamai Sun Kai Hari Kagara A Jihar Neja..
Wasu ‘yan fashi da makami a ranar Laraba da yamma sun mamaye garin Kagara, hedikwatar karamar hukumar Rafi da ke jihar Neja, sun kai hari wani banki tare da kwashe makudan kudade.
Wani shaidar gani da ido ya fadawa gidan Rediyon Prestige cewa wasu mutane dauke da muggan makamai kusan 90 a kan babura 30, sun kaddamar da harin ne da misalin karfe 6:00 na yamma a ranar Laraba.
‘Yan bindigar sun yi ta’asa har zuwa karfe 7:00 na dare a cikin garin Kagara, suna artabu da masu sa kai, wadanda suka yi kokarin bin su da bindigogin Gargajiya.
Mutanen da suka ji rauni suna kwance a babban asibitin Kagara.
Daga Sabiu Danmudi Alkanawi