Kungiyoyi

Wasu Masu Karfi Da Ke Kewaye Da Kai Suna Kare ‘Yan Fashi, Wata Kungiyar Arewa Ta Gayawa Buhari …

Spread the love

Wata kungiyar gamayyar kungiyoyin Arewa (CNG) ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi hankali da mukarrabansa, domin ana zargin wasu masu karfi a cikin gwamnati suna kare wadanda ake zargin ‘yan fashi ne daga kamawa da gurfanar da su.

CNG ta yi kira da a sake kamo wani Abdulmalik Zubairu Bungudu, wanda ta ce, ana zargin ya shirya makarkashiyar hargitsa zaben majalisar wakilai a Bungudu, amma an sake shi “saboda matsin lamba daga masu karfi daga kujerar mulki.”

Yayin da yake magana da manema labarai a Abuja, Kakakin CNG, Abul-Azeez Suleiman, ya ce za a gabatar da koke mai karfi ga Shugaba Buhari don neman “a dauki matakin gaggawa don bankado sunayen mutanen da ke kusa da shi wadanda ke yin zagon kasa ga ayyukan adalci ta hanyar kare wadanda ake zargi da karya doka a kan rashin amincin sa.

Abul-Suleiman, ya bayyana cewa “an umarci reshen jihar ta Zamfara da ya yi aiki da hedkwatar CNG ta kasa don fara gudanar da wata zanga-zanga a Gusau a ranar Litinin, 21 ga watan Satumba don tilasta biyan bukatun don sake kamawa da gurfanar da shi. Dantabawa da sauran mutanen 17 da ake zargi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button