Rahotanni
Wasu Mazauna Jihar Anambra Sun Yi Allah Wadai Da Sarkinsu Da Yaje Ganin Shugaba Buhari A Abuja.
Mazauna yankin Abacha dake jihar Anambra sun fito inda suka yi zanga-zanga kan shiga zugar da sarkinsu, Igwe GB Mbakwe yayi na zuwa ganin shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Zuwan sarakunan ganin Buhari A Abuja dai ya jawo cece-kuce a jihar inda gwamna Willie Obiano ya dakatar dasu gaba daya inda yace sun tafi ganin Buharin ba tare da izininsa ba.
Mazauna yankin Abacha, karkashin jagorancin shugabansu, Mr Ifeanyi Okeke sun bayyana goyon bayansu ga gwamnan inda sukace basa tare da basaraken nasu.
Sun bayyana abinda sarkon nasu yayi a matsayin zagon kasa, kamar yanda Vanguard ta ruwaito.
Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe