Labarai

Wasu ‘yan Arewar da ba sa kishin yankin su waɗanda suke cikin gwamnatin APC ne suka haɗa baki da hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta tsare shugaban ƙungiyar masu kai kayan abinci kudu – sakataren ƙungiyar.

Spread the love

Babban Sakataren kungiyar masu kai kayan abinci kudancin Najeriya na Arewa Ahmed Alaramma ya ce ‘yan Arewar da ba sa kishin yankin su wadanda suke cikin gwamnatin APC ne suka hada baki da hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta tsare shugaban su.

Ahmed Alaramma ya bayyana haka ne Jim kadan bayan fitowar su daga ganawar gayyatar da hukumar DSS din tayi musu.

Alaramma ya ce ba hukumar DSS ce a kashin ta ta gayyace su don ta gana dasu ba, a’a wasu baragurbin ‘yan Arewa dake da karfin iko a cikin gwamnatin APC ne suka shirya ayi wannan gayyatar Wanda daga bisani bayan ganawar hukumar DSS ta sallami sauran mambobin kungiyar taci gaba da tsare shugaban su.

Alaramma yakara da cewa amma wannan mataki da wasu daga nan Arewa marasa kishin yankin su suka sa aka dauka akan su bazai taba sawa su janye kudirin su na daina kai abinci kudancin Najeriya ba harsai mutanen kudancin Najeriya sun dau alkawarin daina cin zarafin ‘yan Arewa mazauna kudancin kasar.

Daga Kabiru Ado Muhd

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button