Labarai
Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a wasu rukunin gidaje a Abuja, sun yi garkuwa da mutanen da ba a tantance adadinsu ba .
Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a wani rukunin gida da ke Chicakore kusa da unguwar Kubwa a karamar hukumar Bwari a babban birnin kasar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan FCT, Josephine Adeh, ta tabbatar da faruwar lamarin, ta kuma ce jami’an da ke yankin suna kokarin tseratar da wadanda aka sace.
Ko da yake ba ta tabbatar da adadin mutanen da aka sace ba, wani mazaunin yankin da ya so a sakaya sunansa, ya ce akwai yara da wata mata da maharan suka tafi da su.
Mazaunin garin ya tabbatar da cewa lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Asabar.