Labarai

Wasu ‘yan Mata sun Kafa Kungiyar daina soyayya a kano

Spread the love

Wasu fusatattun ƴan mata da samari su ka yaudare su a birnin Kano da ke arewacin Najeriya sun bayyana cewa saboda irin yaudarar da kuma cin amanar da samari su ka yi musu ya sanya su ka kafa wata sabuwar ƙungiya mai suna ƙungiyar ƴan mata waɗanda su ka janye daga soyayya.

Shugabar ƙungiyar Juwariyyah Abdullahi Sarki ce ta bayyana haka a lokacin da ta ke tattaunawa da manema labarai a birnin na Kano.

Juwariyyah Abdullahi ta ce babban dalilin kafa wannan ƙungiya shi ne ceto ƴan matan da su ka faɗa a tarkon yaudara da cin amanar samari.

“Dalilin kafa wannan ƙungiya shi ne domin a ceto ƴan mata wanda su ke cikin baƙin cikin yaudarar samarin wannan zamani”

“Wani dalilin kuma shi ne domin su ƴan matan su san cewa za su iya rayuwa ba sai sun yi saurayi ba”

Shugabar ƙungiyar ta ce akwai ƴan mata waɗanda ba za su ƙirgu ba da samarin wannan zamanin su ka yaudare su, wanda hakan ya jefa su cikin baƙin ciki da damuwa tare kuma da yanke ƙauna daga soyayyar baki ɗaya.

“kamar yadda na faɗa maka a baya na ce maka ai yan matan da suka faɗa yaudarar samarin wannan zamani wanda an yi musu ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba harma su ka yanke shawarar su janye daga ita kan ta soyayyar”

Juwariyyah Abdullahi Sarki ta ce wannan ƙungiya da su ka kafa ba sa jawo mutum wai akan lallai sai ya shiga, sai dai idan mace ta faɗa tarkon yaudara har kuma ta yanke ƙauna daga daina soyayyar to a nan ne za su jawo ta ta zama ƴar ƙungiya.

“Bama jan hankalin kowa sai wanda su ka fitar da kansu daga kula samari, su ne mu ke janyo su domin mu haɗa kai mu san abin yi”

Ta ƙara da cewa duk da kafa wannan kungiyar ta su hakan ba ya nuna cewa ba a rasa nagari a cikin Mazan wannan zamanin ba domin akwai waɗanda su ke yin soyayyar kuma sun ci ribarta.

“Ai da ya ke ka san hausawa sun ce ruwan da ya da ke ka shi ne ruwa, saboda haka wasu suna soyayyar kuma ta karɓe su mu kawai muna tafiya ne da waɗanda su ka tsinci kansu a akasin haka”

Hakazalika shugabar ƙungiyar ta ce su a halin yanzu ba su da wani aiki daga sallah sai salati tare kuma da yiwa iyaye biyayya da neman kuɗinsu domin rufawa kan su asiri.

A ƙarshe ta yi kira ga samari da kuma duk wani namiji da ya san ba aure zai yi ba ya ji tsoron Allah ya rabu da ƴan mata, idan kuma ya ƙi ji to babu shakka su na nan su na yin wani shirin taron addu’a ta musamman akan duk namijin da ya zo gurin mace da sunan yaudara Allah ya kafe shi har sai ya aureta.

“Kirana ga Maza shi ne su ji tsoron Allah su daina yaudarar ƴan mata, idan ka san ba aurar yarinya za ka yi ba ka da ka je ka yi ta yaudararta har sai ta ji za ta iya ba da ranta saboda kai sannan ka zame”

“Tabbas ma su yin haka akwai taron addu’a da za mu gabatar nan ba da daɗewa ba, kan cewa duk wanda ya zo gurin mace da niyyar yaudara Allah ya kafe shi sai ya aure ta”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button