Labarai
Wata Kotu A Kaduna Ta Yankewa Matashi Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Laifin Fyade….
Ahmed T. Adam Bagas
Wata babbar kotu dake zamanta a Dogarawa Zariya ta yankewa wani matashi mai Suna Usman Shehu Bashir Hukuncin Kisa ta hanyar Rataya.
Usman Ana zarginsa da Kashe wata Yarinya Mai suna Fatima ta hanyar yimata Fyade.
Tun a Watan da ya gabata ne aka dage zaman kotun domin Tabbatar da laifin mai Laifin.
Wannan mummunan Al’amarin ya zama Ruwa dare a Arewa cin Kasar Nan, Inda wasu suke ganin akwai Sakaci wajen Sashin Shari’a wajen Hukunta masu aikata irin wannan Aika Aikar.