Kungiyoyi

Wata kungiyar Matasan Arewa Ta Nemi Gwamnati Ta Toshe Shafukan Batsa Dan Gyaran Tarbiyya

Spread the love

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe

Wata kungiyar matasan Arewa me suna AYCC ta aikewa da ministan Sadarwa da tattalin arzikin zamani, Sheikh Dr. Isa Ali Pantami bukatar cewa a toshe shafukan batsa a Najeriya.

Kungiyar ta kuma aikewa da ministan yada labarai da Al’adu, Lai Muhammad da irin wannan bukata.Mun fahimci kungiyar ta aike da wannan sako ne ta bakin shugaba ta, Muhammad Ibrahim a yau, 14 ga watan Augusta.

Kungiyar ta nemi da a toshe shafukan dake yada bidiyo da hotunan batsar saboda suna daukar hankulan matasa wanda hakan ke gurbata musu tarbiyya.

Ta kuma yi gargadin cewa idan ba’a dauki wannan mataki ba akwai yiyuwar nan gaba Tarbiyya ta gagara tsakanin matasa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button