Mata iyayenmu
Wata Mata Ta Haifi ‘Ya’ya 15 A Haiwuwa 6..
Matar wadda muka sakaya sunanta tana zaune ne a Alfadarai yankin Anguwan Iya a cikin Birnin Zaria.
A haiwuwar da tayi yau Alhamis ta haifi yara hudu, uku mata daya namiji.
Abin da yafi bawa kowa mamaki shine, ita dai wannan mata kafin wannan haihuwan ta haifi ‘yan uku sau biyu, yan biyu sau biyu da kuma daya sau daya, sai kuma hudun da ta haifa yau.
Kunga kenan a haihuwa Shida wannan Mata ta haifi yara goma sha biyar 15.
Daga Bukar Ali Zaria.