Wata Sabuwa: Duk da an bude iyakokin Najeriya, dokar hana shigo da shinkafa tana nan daram, in ji Shugaba Buhari.
Bude iyakokin Najeriya guda 4 bai Shafi irin kayayyakin da muke iya Samar dasu a Najeriya ba__inji shugaba Buhari.
Bayan kammala halartar zaman majalisar zartarwa ta kasa ta Internet daga Gidansa da ke garin Daura ta jihar Katsina, shugaba Buhari ya bada umarnin bude iyakokin Najeriya guda hudu kacal.
Iyakokin Najeriya guda hudu da shugaba Buhari ya yarda a bude su ne, Seme, Illela, Maigatari da kuma Mfun. Bayan haka shugaban ya jaddada cewa dokar hana shigo da shinkafa da Sauran kayan da Najeriya take da su a cikin Gida tana nan daram.
Buhari ya ce Jami’an tsaron da sukai dako a iyakokin Najeriya ba janyewa za suyi daga iyakokin Najeriya guda hudu da aka bude ba, za su cigaba da zama da kuma sanya idanu akan kama duk wasu kayayyaki da aka haram ta shigo da su cikin Najeriya.
Buhari ya ce an fara bude iyakoki guda hudu ne saboda a ci gaba da shigo da irin kayayyakin da Najeriya ba ta da su a cikin Gidan, Buhari ya ce bude ragowar iyakokin Najeriya kuma zai biyo baya daga karshen watan disamba zuwa junairu Na sabuwar shekara bisa duba ga yadda sakamakon bude iyakokin Najeriya guda hudun ya bayar.
Daga Kabiru Ado Muhd