Labarai

WATA SABUWA: Ganduje baya so Gawuna ya zama minista ya na shirin aikewa da Sunan Rabi’u bichi.

Spread the love

A makon da ya gabata ne shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya mika sunayen ministoci 28, ban da jihohi 11 ciki har da Kano. Wata majiya ta bayyana wa NIGERIA TRACKER cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, na dagewa wajen mika sunan jami’in karbo Sakamakon zabe na jam’iyar APC na a zaben gwamna a Kano, Injiniya Rabi’u Suleiman Bichi.

Sai dai kuma dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a Kano, Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna, yana kuma matsa lamba kan a saka sunansa a cikin jerin sunayen da za a mikawa majalisar dattawa domin tantancewa.

Majiyar ta kara da cewa a yanzu dan takarar Gwamna na jam’iyyar APC yana aikewa da jakadu zuwa ga Gwamna Ganduje, inda ya bukace shi da ya mika sunansa a matsayin wanda za’a nada ministoci daga Kano.

Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya yi alkawarin ba Kano mukamai biyu ministoci daya, daya na shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, da daya daga sansanin Gandujiyya na tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje. Tun da Ganduje bai cike Sharadin da ake bukata na zama minista a majalisar ministocin Shugaba Tinubu ba, shugaban kasar ya ba shi damar nada minista, wanda a yanzu haka ya janyo ce-ce-ku-ce a fagen siyasar tsohon Gwamna Ganduje.

Majiyar ta kuma sanar da NIGERIAN TRACKER cewa idan shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu zai mika sunayen ‘yan takara na gaba daga Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, shugaban jam’iyyar NNPP na kasa da kuma wani mutum daya da tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje zai zaba.

Wata majiya ta sanar da NIGERIAN TRACKER cewa sansanin rusasshiyar jam’iyyar Action Congress Of Nigeria a Kano, karkashin jagorancin shugaba Tinubu a zaben 2007 da 2011, na dagewa wajen nada dan takarar gwamna a jam’iyyar a 2011 kuma tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano. Injiniya Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo.

Dalilan da tsaffin jiga-jigan jam’iyyar ACN suka bayar na cewa shugaba Tinubu ya nada Injiniya ATM Gwarzo a cikin majalisarsa, shi ne, shugaban kasa Tinubu ya yi fice wajen ba da lada, kuma kasancewarsa babban amininsa, Injiniya Gwarzo yana cikin wadanda suka fi cancantar zama minista a Kano.

Don haka ana sa ran shugaba Tinubu zai tuntubi tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, duk da cewa a halin yanzu yana PDP, saboda rawar da ya taka wajen kafa APC a 2011.

Majiyar ta kuma bayyana cewa, shugaba Tinubu baya gaggawar nada ministoci daga Kano, domin nadin na iya samun albarkar Sarkin Kano na 14, wanda shugaba Tinubu zai iya tuntubar shi kafin ya kammala jerin sunayen daga Kano.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button