Rahotanni

Wata Sabuwa: Kamata Yayi Farashin Litar Man Fetur Ya Tsaya A Naira 76, Daidai Da Shekarun Buhari 76 — Inji Guru Majaraji.

Spread the love

Wanda ya kirkiro addinin ‘One Love Family’, Sat Guru Maharaj Ji, ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya zaftare farashin litar fetur, saboda kuncin rayuwa da ya yi katutu a rayuwar yan Najeriya.

Da ya ke bayani cikin wata takardar da ya fitar domin taya yan Najeriya murnar shekara 60 da samun yanci, Maharaj Ji ya ce kamata ya yi litar mai ta tsaya farashi daya da shekarun Buhari, wanda ya ce shekarar sa 76.

Na sha cewa a matsayin Najeriya kasa mai arzikin fetur, kamata ya yi farashin kowace lita ya rika tsayawa daidai da yawan shekarun duk Shugaban kasar da ya hau mulki.

Misali, idan shekarun shugaban kasa 76, to litar fetur kada ta wuce naira 76.

Cikin watan da ya gabata an kara wa litar fetur kudi zuwa naira 147 a farashin sari. Su kuma dillalan mai su ka yi na su kari, inda a gidajen mai ake sayar da lita daya naira 160 zuwa 161.

Sat Guru ya ce yan Najeriya na da hujja da dalilin nuna fushi da bacin ran su, ganin yadda shugabanni ke zaluntar su, ta hanyar tauye masu hakkin cin moriyar albarkatun cikin kasa da Allah ya wadata Najeriya da su.

Duk da haka ya ce ba ya goyon bayan zanga-zanga da yajin aiki. Ya bada shawarar cewa kamata ya yi gamayyar kungiyoyi kwadago su zauna neman sulhu da gwamnatin tarayya domin a samu mafita ba tare da talakawa sun kuntata ba.

Yayin da ya ke kara jinjina cewa tattaunawa a kan teburin shawara ne mafita, ya ja hankalin gwamnati da ta tuna nauyin dimbin milyoyin al’ummar da ke kan ta, wadanda baya ga neman saukin kuncin rayuwa, ba su bukatar komai a wajen gwamnati.

Gwamnati ta rika sassauta wa marasa galihu ta hanyar tausayawa, jinkai, agazawa da tallafa masu da kayan rage radadin talauci da kuncin rayuwa.

Guru ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta kwace harkokin wutar lantarki daga hannun wadanda ya kira kaskar da ke shanye jinin tattalin arzikin jama’a.

A karshe ya ja hankalin shugabannin coci-coci cewa dokar CAMA ba abin tsoro ba ce, matukar shugaban coci ya san ba aikata harkalla ya ke yi da kudade ba.

Daga Comr Haidar Hasheem Kano

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button