Rahotanni
Wata Sabuwa: Karya ne bamu kama Rahama Sadau ba, in ji ‘Yan Sanda.
Hukumar ‘yan Sandan Najeriya reshen Babbban birnin tarayya Abuja ta karyata jita jitar da ake yadawa cewa sun kama jarumar fina finan Hausa Rahma sadau.
Hukumar yan sandan ta ce bata kama Rahma sadau ba.
Hukumar yan sandan ta ce tana Kira ga jama’a dasu daina saurin yarda da duk labarin da bashi da tushe don gujewa fadawa cikin laifin masu yada labaran karya wadanda a yanzu ake kan yaki dasu ta kowacce irin fuska.
Daga Kabiru Ado Muhd