Wata Sabuwa Kawo yanzu mutun 83,719 suka Ratta6a hannu kan takardar Neman kasar burtaniya tasama Nageriya Takunkumin..
Kawo yanzu Takardar neman kasar Burtaniya da ta sanya takunkumi ga mambobin gwamnatin Najeriya da rundunar ‘yan sanda saboda keta hakkin dan adam kan harkar #ndSARS an sanya hannu kan mutane 83,719. Wannan ya kasance ne tun daga karfe 12.51 na safiyar ranar Laraba lokacin da wakilinmu ya ziyarci shafin koken. Takardar karar wacce wani mai suna Silas Ojo ya kirkiro, na neman samar da sa hannu 100,000. “A sa hannu na 100,000, za a yi la’akari da wannan koken don muhawara a Majalisar,” daga Nan zuwa Afrilu 20, 2021.
Takardar koken ta shafin intanet na gwamnatin Burtaniya da majalisar dokoki ta karanta cewa, “An yi zurfi ciki game da rahotannin rundunar‘ yan sanda ta Najeriya (SARS) da ke aikata ayyukan da suka saba wa doka da kuma take hakkin dan Adam, haka kuma an samu rahotannin ‘yan sanda na yin harbi kan masu zanga-zangar da ke kiran a Rushe SARS “Aiwatar da takunkumi kan Gwamnatin Najeriya da jami’ai. Ya kamata Gwamnati ta bincika yin amfani da sabon tsarin takunkumin da ke ba da dama ga daidaikun mutane da hukumomin da ke keta haƙƙin bil’adama a duk duniya,